Topha Kamata Ka Hakura Ɗa Mulkin Kano Bayan Ka Janye Hawan Sallah Da Za'kayi
Wata Sabuwa: An Fara Shawartan Sarki Aminu Ado Bayeɍo Ya Hakura Ɗa Mulkin Kano Bayan Ka Janye Hawan SALLAH
An Fara Shawartan Sarki Aminu Ado Bayeɍo Ya Hakura Ɗa Mulkin Kano Bayan Ka Janye Hawan Sallah
Bayanai sun fara yaduwa a cikin al’umma tun bayan da mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya janye daga shirin gudanar da Hawan Sallah. Wannan matakin da ya dauka ana kallonsa a matsayin wani yunkuri na tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, inda ya bar wa Muhammadu Sanusi II damar jagorantar bikin ba tare da wani cikas ba.
Wannan batu ya janyo cece-kuce, musamman ganin irin halin da masarautar Kano ta tsinci kanta a ciki a 'yan watannin nan. Yayin da wasu ke ganin matakin na Aminu Ado Bayero a matsayin na kishin kasa da kokarin hana rikici, wasu kuma na bayyana shi a matsayin janyewa daga wata takaddama da ke kara kamari a siyasar masarautar Kano.
Hawan Sallah na daya daga cikin manyan al’adun da suka dade suna gudana a Kano, inda sarki ke jagorantar dandazon al’umma da fursunoni a cikin birni don nuna farin ciki da cika azumin watan Ramadan. A wannan karo, dai, janyewar Aminu Ado Bayero ya bai wa Muhammadu Sanusi II damar yin hakan ba tare da wata tangarda ba, lamarin da zai iya zama alamar wani sabon salo a tsarin mulkin masarautar.
Yanzu dai idanu sun koma kan yadda za a gudanar da wannan hawan Sallah da kuma irin tasirin da wannan mataki zai yi a makomar masarautar Kano. Za a ci gaba da bibiyar al’amura don ganin ko wannan mataki zai haifar da daidaito ko kuma zai kara dagula al’amura a siyasar sarauta a jihar.
MUNGODE DA ZIYARAR GIDAN NAN DOMIN NISHADI ILIMANTARWA NISHADI A KASANCE DAMU KANA KUYI SHARING PLEASE.

Post a Comment