Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajeeun: Kap Kannywood Babu . Mai Iya Maye Gurbinta,Saratu Gidado
Saratu Gidado: Kannywood Baxa Ta Iya Maye Gurbinta Da Wata ba. Anyi Babɓan Rashi.
Saratu Mohammed Gidado, wadda aka fi sani da Daso, fitacciyar jaruma ce a masana’antar fina-finan Hausa, wato Kannywood. An haife ta a ranar 17 ga Janairu, 1968, a unguwar Chiranchi, karamar hukumar Gwale, cikin Jihar Kano.
Ta fara harkar fim a shekarar 2000, inda fim ɗinta na farko shi ne “Linzami Da Wuta” da kamfanin Sarauniya Movies ya shirya. Ta shahara wajen fitowa a matsayin muguwar mace, musamman mai yawan hayaniya da rigima a fina-finai. Wasu daga cikin fina-finan da ta fito sun haɗa da Nagari, Gidauniya, Mashi, Sansani da sauransu.
A shekarar 2016, an naɗa ta Jakadiya ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wato mai kula da wasu harkokin masarauta na musamman.
Saratu Gidado ta rasu ne a ranar 9 ga Afrilu, 2024, tana da shekara 56. Rahotanni sun ce ta ci Sahur da safe saboda azumin Ramadan, sannan ta kwanta barci, amma ba ta farka ba.
An yi babban jimami a Kannywood da ma fadin Najeriya bisa rasuwarta, inda aka yaba da rawar da ta taka a harkar fim da kuma yadda ta ba da gudunmawa wajen ci gaban al’adun Hausawa.
Allah ya jikan Daso, ya gafarta mata.
MUNGODE DA ZIYARAR GIDAN NAN DOMIN NISHADI ILIMANTARWA NISHADI A KASANCE DAMU KANA KUYI SHARING PLEASE.
Post a Comment