Header Ads

Topha Asiri Ya Tonu, Sarkin Waka Kayan Lefe Ma Bashi Kaci Inna Ga Mota

 Har Yanzu Ina Bin Naziru Sarkin Waka Bai Biya Ni Kuɗin Lefen Aurensa Da Na Haɗa Masa Ba, Cewar Rashida Mai Sa’a



Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa’a, ta bayyana cewa har yanzu ba a biya ta kuɗin lefen auren da ta taimaka wa mawaki Naziru Sarkin Waka wajen haɗawa ba. Ta ce ta yi aikin da zuciya ɗaya, amma har yau bai cika alkawarin da ya dauka na biyanta ba.
‎Rashida ta yi wannan bayani ne cikin wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, inda ta bayyana yadda ta tsaya masa lokacin da aka fara shirye-shiryen aurensa, amma yanzu ya kasa waiwayar ta ko godiya, bare ya biya bashin da ya ci.
‎“Na yi lefe da hannuna, na fita na nemo kayan komai daga kasuwa har da na miji. Amma yanzu bai ma damu da jin halina ba, balle biyan bashin,” in ji ta cikin takaici.
‎Wannan bayani ya haifar da cece-kuce a tsakanin masoyan jaruman biyu, inda wasu ke ganin ya kamata Naziru ya fito ya yi bayani ko ya warware matsalar a tsakaninsu da mutunci.

No comments

Powered by Blogger.