Header Ads

GWANIN SHA'AWA:Gwambatin Kano Tare Da Jagoran Kwakwasiya' Bankwana ɗaliban Da Ta Dauki

 Da Dumi Dumi: Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf kenan tare da jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso lokacin da suke bankwana da kashin farko na ɗaliban da Gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin karatun su.

Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ne ya ɗauki nauyin karatun nasu, zuwa kasashen waje domin yo digiri na biyu, ɗalibai su 1,001.

A cewar Gwamnan kashin farko ne suka tafi yayin da sauran suma zasu tafi a sauran jiragen masu zuwa.

Gwamnan ya kuma baiwa ko wanne ɗalibi kyautar Dala 200 na kashewa tare da sanya musu albarka da fatan yin karatu mai albarka.

A yayin rakiyar jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana jin daɗin kan wannan kyakkyawan aiki da Gwamnan yayi.

Wane fata za kuyi masa ?

No comments

Powered by Blogger.