Tirkashi Auren Wanda Bai Dace Ba A Lokacin Da Ya Dace Shine Babban Matsalar Rayuwan Aurena
Topha Auren Ameena:Nayi Aure to Lokacin Da Ya Dace Da Wanda Bai Dace Ba Kalubale.
Ameena Rani, wadda aka fi sani da Jamila Labarina, ta yi karin bayani kan furucinta na cewa ta auri mutumin da bai dace ba a lokacin da ya dace.
Ta bayyana hakan ne a dandalin Hadiza Gabon, inda ta ce wannan furuci nata ya haifar da cece-kuce har masoyanta suka rika jan hankalinta kan batun. Saboda haka ta ga dacewar ta fito ta yi karin haske.
A cewar Ameena, kalaminta na cewa “she got married to a wrong person at the right time” ba su nufi cin mutunci ko zagi ga wani ba. Abin da take nufi shi ne, da ace Adam A. Zango shi ne wanda ya dace da ita, to da yanzu suna tare a matsayin ma’aurata. Haka zalika, da ita ce ta dace da shi, da yanzu suna tare.
Ta kara da cewa abin da ta kira “a lokacin da ya dace” yana nufin ta yi aure tun tana da karancin shekaru, domin a cewarta ko shekara 20 bata cika ba lokacin da aka daura mata aure, sannan kuma ta samu karuwa.
A baya jameela labarina ta Yi marmarin komawa gidan uban yaronta haidar A zango dalilin da ya ja hankalin masoyanta a kafafen sada zumunta kenan#kannywood_kd #kannywood



Post a Comment