Header Ads

Rahama Sadau ta bayyana yadda take ji idan tayi abunda ya jawo CeCe kuce ga al'umma

Rahama sadau ta bayyana alakarta da Ali Nuhu+Rahama tana daya daga cikin Jaruman kannywood da take yawan yin abubuwan da suke jawo hankalin mutane a kafar sada zumunta.


Rahama Sadau ta bayyana yadda take ji idan tayi abu wanda ya jawo CeCe kuce ga al'umma

Rahama tana daya daga cikin Jaruman kannywood da take yawan yin abubuwan da suke jawo hankalin mutane a kafar sada zumunta

A cikin wannan tayi bayyanin abubuwan da sai sun baku mamaki.

 






Rahama sadau ta bayyana alakarta da Sarki Ali nuhu 

Abubuwan da ke cikiKin taba da na sanin  yin wani abuMenene alakari da Ali NuhuRahama Sadau ta bayyana mutane ukku da ba za ta manta da su ba a kannywood

Shaharariyar jaruma masanantar kannywood Rahama sadau tayi fira da gidan jaridar TRTAFRIKA inda ankayi mata tambayoyi sosai akan abunda ya shafi rayuwarta.

Kin taba da na sanin  yin wani abu?

Da zarar abu ya faru da ni nake daukarsa a matsayin darasi , saboda haka babu batun  na yi da  sani  kawai dai nayi abin da ya jawo  magana,  sai na dauki darasi  na ci gaba da rayuwarta shikenan.

Sai kuma a kula da gaba, abin da nake gaya wa kaina kenan..

Rahama sadau ta bayyana alakarta da Ali Nuhu Hoto: Instagram/Ali nuhu, Rahama sadau

Gaya mana mutum ukku da ba za ki manta da su ba a kannywood?

“Idan kace na fadama zan iya cewa Ali Nuhu, Ali Nuhu, Ali Nuhu amma bari a barshi matsayin daya Ali Nuhu, yaseen auwal akwai Ali Nuhu..

Menene alakari da Ali Nuhu?

“Rahama sadau : Ali nuhu uban gida ne, gwani  ne kuma mai gidan kowa , kuma ya bani gudunmuwa sosai a rayuwata kusan in ce kashi Casain zuwa dari  na rayuwata a kannywood da yadda na taso, da kula dani.

“Ya bani kariya a matsayin  uban gida  kuma na gode masa kuma a kowacce  masana’anta idan ka shiga dole kana bukatar wanda zai dora a turba saboda haka ina ganin girmansa sosai

No comments

Powered by Blogger.