Tirkashi Nasha Da karr A Saudiya Baayan An Yankemin Hukunci Kisa Cewar Adaman Kamaye
Wata sabuwa Kalli hirar adama` yadda Aka Yanke Min Hukuncin Kisa A Saudiyya Da Yadda Allah Ya Kuɓutar Da Ni.
Yadda Aka Yanke Min Hukuncin Kisa A Saudiyya Da Yadda Allah Ya Kuɓutar Da Ni, Cewar Adama Ta Shirin ‘Daɗin Kowa’
Zuwaira Saleh Pantami, wadda aka fi sani da Adama a cikin shirin wasan Hausa mai dogon zango, wato ‘Daɗin Kowa’, wanda gidan Talabijin na Arewa 24 ke nunawa, ta bayyana yadda ta taka sawun ɓarawo a ƙasar Sa’udiyya, har aka yanke mata hukuncin kisa.
A wata tattaunawa da Dandalin Hadiza Gabon na ‘Gabon’s Room Talk Show’ ya yi da ita, Zahara’u, ko kuma a ce Adama, ta bayyana cewa an taɓa yanke mata hukuncin kisa tare da wasu mata bakwai, amma aka zartas da hukuncin kisa akan sauran bakwai ɗin, ita kuma ta kuɓuta.
A cikin bayanin da ta yi Hadiza Gabon, wanda ta nuna cewa ita ba laifi ta yi ba, sawun ɓarawo ta taka, ta ce Allah ne ya kuɓutar da ita, saboda ba ta aikata laifin da aka kashe sauran ba, saboda su sauran duk sun aikata laifin da aka tuhume su da aikatawa.
Adama, wadda ta ce ‘yar’uwar tsohon Minista Ali Pantami ce ta jini, ta bada labarin yadda abin ya faru, ta ce da farko ta je Umra, amma sai ta tafi da irin tarkacen kayyayakin da ake tafiya da su daga nan Najeriya don ta sayar a can.
Ta ce, “na tafi da irin su daddawa, kuka, kuɓewa, goro da sauran su. To da na sayar sai na ga ribar da na samu har ta nunka jarin. Sai kawai da na dawo Najeriya sai na riƙa sarin irin waɗannan kaya, ina tafiya da su Saudiyya, ina sayarwa, ina dawowa ina sake saye na koma.”
Ta ce ta shafe lokaci mai tsawo ta na yin haka, har sai ranar da aka kama ta, wanda daga nan ne ba ta sake yi ba.
Ta ce a wani zuwa da ta yi, wata rana ta na cikin birnin Riyad, sai ta yi kaciɓus da wata ƙawar ta ‘yar asalin Sudan.
Adama ta ce ƙawar ta na zaune a wani gari ne mai suna Idesa, wanda ke gaba da Riyad, inda ita Adama ɗin kan je ta na kai masu kuka, daddawa, kuɓewa da sauran su. A can ta san ƙawar, har su ka shaƙu.
“To amma fa rabon da mu ga juna an kai shekaru huɗu. Sai ta ce min ita yanzu a Jedda ta ke zaune, kuma ta je
GA BIDIYON👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

Post a Comment