Shakka Babu" Rarara Bashi Da Laifi Wallahi Akan Kalamansa. Buhari yaci amanar Yan Nigeria
Wlh duk abinda Yaki faruwa Bazamu ga laifen Rara ba saboda Buhari yaci amanar Yan Nigeria
Ayi hakuri maganar rarara gaskiya ce.Tabbas naji dukkanin abinda rarara yafada ma yan uwana yan jaridu,akan matsalar kasar nan Saidai nasan wasu abun bazai musu dadi ba, kuma abinda rarara yafadi shine zance na Adalci maganar gaskiya tsohon shugaban kasa (Buhari)tare da mukarraban sa sune suka kashe kasar nan a zahirin gaskiya.
Wallahi bana kallon rarara a matsayin butulu saboda a maganar sa ance yan PDP sune suka kashe kasar nan a farko tom meyasa baza'a fadi abinda Buhari yayi ba,kuma rarara bafa zagin Buhari yayi ba, gaskiya ce a siyasa yafada, wallahi bazaka kara tabbatar wa da abinda rarara yake fada ba,saika yi zama da masu iyali a wannan lokaci damuke cikin ta.
Idan gaskiya tazo a fade ta,anga irin barnar da'aka dinga yi a gomnatin baya,banda daruruwan jama'a da'aka dinga kashewa tare da rabasu da dukiyar su, meyasa bazamu fadi gaskiya ba,shin abubuwan da rarara ya fadi karya ne? Koko kawai saboda wasu dalilai zaisa wasu zagin sa dakuma cece kuce akan abinda yake zahiri yakamata mu hankalta kwarai da gaske,amman maganar kashe kasar nan lokacin Buhari kasar nan ta shiga wani yanayi mai muni Wanda shine ya haifar da dukkanin abubuwan dasuke faruwa
Yakamata dai mudawo hayyacin mu yan kudu idan kana shugaba,bakayi musu aiki ba koka gaza a wasu bangaren zasuyi kokarin fadi,amman mu yan Arewa kullum sai ace kaza a rufe mana baki ba'a son muyi magana,bayan kowa yasan gaskiya ce.
Allah kasa mudace kakawo mana dauki a kasar mu Nigeria,kuma kakawo mana zaman lafiya a yankin mu na Arewa yaa Allah.
Ga Cikekken Maganarsa👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
.jpg)
Post a Comment