Header Ads

Topha Ina Masoyana Dan Allah Kusaka Ni Addu'arku Matar Aure Da Zàmu Rayu Har Abada

 Ina Bukatar Matar Aure Wacce Xamu Rayyu Tare Har Abada Masoyana Kú Sakani A Addu'arku



DAN ALLAH KU SAKA NI A ADDU'ARKU ALLAH YA BAYYANA MIN MATAR DA ZAN AURA WACCE MUTUWA CE KAƊAI ZA TA RABA MU, CEWAR JARUMI ADAM A. ZANGO

Fitaccen Jarumi a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya nemi al'ummar musulmai su taya shi da addu'a Allah Ya ba shi matar aure wacce ba za su taɓa rabuwa ba har abada.

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito A. Zangon na bayyana hakan ta cikin shafinsa kamar yadda ya ce:

"Dan Allah ku saka ni a addu'arku Allah Ya bayyana min matar da zan aura a cikin wannan wata mai albarka Daren Lailatul Qadir. Matar da zan yi alfahari da ita Duniya da Lahira. Allah Ya sa mutuwa ce kaɗai za ta raba ni da ita". Ya ce.

Idan jama'a ba su manta ba, an sha ruwaito labaran mutuwar aurarrakin da Jarumin yayi wanda har ta kai ga mutane na jifansa da "mai auri saki" wanda shi da kansa ya sha fitowa kafar sadarwa ta zamani yana kare kansa daga zarge-zargen da al'umma ke yi masa tare da bayyana hakan a matsayin wani babban abin baƙin ciki da damuwa da ke damunsa sosai.

No comments

Powered by Blogger.